2016, na cikin shekarun da masu ruwa da tsaki a finafinan Hausa Kannywood ba za su manta da ita ba. Abubuwa da dama sun faru a shekarar — masu dadi da marasa dadi — wadanda suka yi tasiri kan yadda ake tafiyar da wannan babbar harka.
Tun a farkon shekarar ne, watau a watan Fabrairu, Kannywood ta soma gamuwa da babban gibi sakamakon mutuwar fitacciyar jarumar nan Aisha Dankano. Aisha, wacce aka fi sani da Sima ta yi fice wajen amfani da kalmomi masu cike da hikima da kuma ban dariya a finafinan Hausa, wadanda da wuya a samu wanda ko wadda za ta maye gurbinta a wannan bangare.
Har ila yau, wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar sun yi rashin iyayensu a cikin wannnan shekara, da suka hada Babban Furodusa, Abdul Amart Mai Kwashewa da ya yi rashin mahaifiyarsa, sai kuma jarumi Shu’aibu Lilisco da shi ma mahaifiyarsa ta kwanta dama.
Ginin Alkaryar Fim
Batun ginin alkaryar fim a 2016, yana cikin manyan labarum da suka tayar da hazo a tsakanin masu bibiyar harkokin finafinan Hausa, da ma wadanda harkar bat a dame su ba. Shafukan sada zumunta sun bada muhimmiyar gudunmawa wajen dakatar da ginin, da yake dubun dubatar al’ummar musamman da Arewacin kasar nan sun nuna rashin goyon bayansu game da wannan shirin da Gwamnatin ta yi aniyar kaddamarwa.
Shugaban Hukumar tace finafinai ta jihar Isma’ila Na’Abbah Afakallah, ya shaida min cewa alkaryar za ta kasance ta farko a Nijeriya, yana mai cewa masu shirya fina-finai daga kowacce kusurwa ta duniya za su iya zuwa Kano domin yin amfani da ita.
A cewarsa “Za a kashe sama da Naira biliyan uku wajen gina alkaryar, kuma ana sa ran fiye da mutum 10,000 za su samu aiki idan aka kammala aikin.”
Sai dai ce-ce-ku-ce da kuma muhawarar da aka rika tafkawa a shafukan sada zumunta na zamani a kan dacewa ko rashin dacewar gina alkaryar da kuma caccakar da shirin ya sha a wajen wasu Malamai sun tilasta wa gwamnatin tarayya soke shi.
Zargin Luwadi
Al’amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda suka kamata a Kannywood, inda aka rika sa ran fitar da manya manyan finafinai, wasu sun yi ma’ana da tasiri, yayin da wasu kuma babu komai a ciki sai shirme. Har zuwa sabbin zarge-zarge da suka sake bullowa.
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta soke shirin gina alkaryar fina-finai ne dai aka rika yin musayar yawu tsakanin wasu ‘yan fim da malamai, inda aka jiyo wasu malaman na cewa wasu ‘yan fim din ‘yan luwadi ne, yayin da wasu ‘yan fim din suka rika yin gugar zana ga malaman.
Sai dai da alama batun zargin luwadin da aka yi wa ‘yan Kannywood din ya shiga kunnen jama’a, lamarin da ya harzuka ‘yan fim da dama.
A wata hira da fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi da gidan talabijin na DITB da ke Kaduna, ya musanta zargin yin luwadi, inda ya dafa Al-Kur’ani, sannan ya sha rantsuwa cewa bai taba yin luwadi ba, kuma shi ma ba a taba yi da shi ba, yana mai cewa idan har kalamansa babu gaskiya a ciki, Allah Ya halaka shi.”
Shi ma jarumi Baban Chinedu, a wani bidiyo da ya fitar, ya musanta zargin. Inda ya yi rabtsuwa cewar, “Wallahil azimun! Wallahil azimun ni ban taba luwadi ba, kuma ba a taba luwadi da ni ba!”
Abokin aikinsa ma, Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Naburaska, ya caccaki mutanen da suke yi musu kazafi, yana mai cewa nan gaba kadan zai fito da shaidun da za su tozarta mutanen.
Korar Rahma Sadau
Masu nazari a harkar finafinan Hausa sun yi ittifaki cewa rabon da Kannywood ta shiga rikici kamar wanda Rahma Sadau ta janyo mata tun bayan faifan bidiyon Rahamatsaraicin Maryam Hiyana da ya fita a shekarun baya. Sakamkon fitowa da ta yi a faifain bidiyo tare da wani mawakin Ingausa mai suna Kilasik.
A cikin wakar mai suna ‘I Lobe You’ wacce ke da tsawon minti hudu da dakika 19, an ga Rahma a A wurare da dama tana jingina a jikin mawakin, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki na Kannywood da ma al’umma baki daya.
Hakan dai ya sa kungiyar masu harkar shirya finafinan Hausa, MOPPAN, ta sanar da korar ta daga Kannywood kwata-kwata, hukunci da a lokacin wasu ke ganin ya yi tsauri ainun.
Jarumar ta nemi gafara kan wannan batu kodayake ta ce ba zai yiwu ta yi aiki ba tare da ta taba wani ba.
Gasar Kaddamar Da Gidauniya
Wani abu da ba za a manta da shi ba a wannan shekarar game da ‘yan Kannywood shi ne yadda wasunsu suka mayar da hankali wajen taimakawa jama’a ta hanyar kafa gidauniya.
Jarumai irinsu Adam A. Zango da Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon sun kafa gidauniyoyi domin tallafawa gajiyayyu da mabukata.
Gabon ta bayyana da cewa, “Yana da kyau mutum ya nuna godiya ga Allah bisa baiwar da ya yi mana, sannan mu nunawa marasa karfi cewa Allah yana tare da su.”
Ita dai wannan jaruma ta bayar da tallafi sau da dama ga ‘yan gudun hijrar da suka bar gidajensu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wadanda yanzu haka suke sansanonin ‘yan gudun hijira.
Baya ga haka, tana taimaka wa daliban kananan makarantu da litattafai da sauran kayan koyon karatu.
Shi ma a nasa bangaren, Adam A Zango ya kafa wata gidauniya mai suna Zango Interbention Initiatibe.
A cewar jarumin, gidauniyar za ta rika bayar da taimako ga marasa galihu da marasa lafiya da ‘yan gudun hijira da marayu da zawarawa.
Zango ya ce zai samu kudin gudanar da gidauniyar ne ta hanyar shirya bukukuwan rawa a dukkan jihohin Nijeriya wanda zai soma a watan Janairu mai zuwa.
Ita ma Nafisa Abdullahi ta kafa irin wannan gidauniya mai suna The Lobe Laugh Foundation, wacce ta ce za ta mayar da hankali ne kan nuna kauna da tallafi ga marasa galihu da mata da marayu da ‘yan gudun hijira. Har ma ta gudanar da wani bikin na musamman neman tallafi daga masu hannu da shuni wadanda suka taimaka domin harkokin gudanarwar gidauniyar su tafi yadda ya kamata.
Masu fashin baki kan yadda lamura suke tafiya a Kannywood sun yi san barka ga wannan kokari da jaruman ke yi na taimaka wa al’uma.
Malam Ibrahim Sheme, wanda ya dade yana tsokaci kan Kanyywood, ya ce matakin zai inganta dangantakar da ke tsakanin jaruman da al’ummar da ke yi musu kallo a matsayin masu wargaza tarbiyya.
Ya kara da cewa, “Wannan mataki yana da kyau amma ina ganin ba shi da tsari. Ya kamata jarumai kamar goma wadanda ke da irin wannan aniya su hada kungiya da za ta rika aiwatar da irin wannan shiri, ba kowa ya yi gaban kansa ba.”
Yanzu dai mun yi bankwana da shekarar 2016 mun shiga sabuwar shekara, babu makawa cewa harkokin da ake gudanarwa a Kannywood za su ci gaba da jan hankalin jama’a da kuma yin tasiri a rayuwarsu.
0 Response to "Muhimman Abubuwan Dasuka Faru A Masana'antar Kannywood A Shekarar 2016 "
Post a Comment