Takai Taccen Tarihin Mawaki Nura M Inuwa Tattaunawa Kai Tsaye Tafeda Jarumi Abas Sadiq Cikin Shirin Gani Da Idonka.
ABBAS SADIQ : Da farko dai masu Sauraro zasuso suji takai taccen tarihinka?
Nura M Inuwa : Da farko dai sunana Nura Musa Inuwa wanda a yanzu akafi sani da Nura M Inuwa, Ni Haifaffen Garin Kano ne Gommaja Karamar Hukumar Dala.
Nayi Makaranta na na primary school a masaka special primary school daganan na wuce Gommaja two inda inda acan nayi secondry school dina daga nan kuma cikin ikon ubangiji banci gaba ba, Daganan sai na fara harkar waka.
ABBAS SADIQ : Nura M Inuwa me yaja hankalin kane har ka fara harkar Waka?
Nura M Inuwa : Aah! Alhamdulillahi Nidai tun farko bani da wani dalili da yaja hankalina na fara harkar waka, sabo da ya samo asaline tun ina yaro ni kaina haka kawai inayin waka haka kuma idan akan batamun raj nakanyi waka domin in huce bacin ran nan da akamun hakama idan an faranta mun nakanyi waka.
Ta yadda tun bansan kalar ko launin wakaba da yadda take nidai kawai inayi, daga baya kuma saina sawa raina cewa inason in fara waka, ina girma ina girma sai nazo na fara Makaranta, Sabo da haka Allah cikin ikon sa sai na fara waka a Makaranta inda nakanyi waka ta Yabo musamman in ana Maulidi inzo in rera a haka a haka abu yanaci gaba.
Kancewar ba wakar Yabon na fara yiba, Sai akazo idan na kalli Film "Misali" Ace wannan Film din na daya ne lokacin ana yin film pert 1 and 2 to a lokacin sai ya zamana ina iya kirkirar waka ta kaina idan na kalli film na daya kuma ya burgeni to sai in kirkiri waka tawa ta kaina wacce nake ganin itace zata zama ci gaban wannan shirin film din.
Da haka da haka inayi Allah cikin ikonsa har nazo na fara Waka dana farane kuma sai na fahimci cewa zan iya daukar waka a mastayin haryace ta tura sakon ni na fadakarwa sannan kuma zan iya rikanta a matsayin sana'a kamar yadda take yanzu a wurina.
Wannan Shine Kadan Daga Cikin Abunda Muka Dan Tsakuro Muku Dangane Da Tarihin Mawaki Nura M Inuwa, Akwai Yiwuwar Ci Gaba Da Kawo Muku Wannan Tattaunawa Nan Bada Jimawa Ba.
0 Response to "Kannywood: Cikakken Tarihin Nura M Inuwa "
Post a Comment