Kannywood: Jarumi Zaharaddeen Sani Ya Shirya Wani Sabon Fim Mai Nuna Rikicin Boko Haram

Shahararren jarumin nan kuma furodusa Zaharadeen Sani ya ce ya samu amincewar hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS tare da hukumar tantance fina finai ta kasa domin ya shirya fim da ke nuna rikicin Boko Haram.

A wata hira da yayi da jaridar Premium Times, Zaharadeen ya ce ya fuskanci kalubale da farko domin hukumar tantance fina finai ba ta amince da fim din ba saboda irin tufafin ‘yan ta’addan da aka yi amfani da su da kuma bindigogi da khakin sojoji.

Ya ce haka kuma ya samu gayyata daga DSS domjn ya zo ya kare dalilansa na shirya fim din.
Zaharadeen ya ce ya shirya fim din ne saboda ya nunawa mutane illar da rikicin Boko Haram ya haifar a kasar nan, wanda da shi ne yake kwana da shi yake tashi.

Fim din mai suna ABU HASSAN dai ana hasashen cewa ba a taba yin irin sa ba a Kannywood.

Labarin ya nuna wata kungiyar ta’addanci da ta addabi mutane wacce sojoji suka ci lagwanta daga karshe.

0 Response to "Kannywood: Jarumi Zaharaddeen Sani Ya Shirya Wani Sabon Fim Mai Nuna Rikicin Boko Haram "

Post a Comment