News: Fitaccen Dan Wasan Kwallon Kafar Nan Wato Ahmad Musa Ya Saki Matar Sa

Akwai maganganu daga majiya mai karfi kan cewar fitaccen dan wasan kwallon nan na kulob(club) din Leicester City FC wanda kuma yake a mazaunin mukaddashin kaptin din kulob din Super Eagles wato Ahmad Musa ya saki matarshi Jamila biyo bayan cece-kucen da ya shiga tsakaninsu a farkon watannan.

Takaddamar dai ta samo asali ne biyo bayan kara auren da shi wannan fitaccen dan kwallon ke shirin yi na wata budurwa mazauniyar Lagos haifaffiyar garin Calabar mai suna Ejue Juliet Adeh inda tuni shirye-shiryen auren na su yayi nisa.


Kamar yadda majiyar ta bayyana, dan kwallon ya saki matar tashi Jamila saki uku bayan kamarin da cece-kucen na su yayi. Majiyar ta tabbatar da cewar yanzu haka Jamila ta koma gida can birnin Kano biyo bayan sakin.

A makon da ya gabata ne dai akai ta yada rade-radin cewa Ahmad Musa ya bugi matar tashi dangane da takaddamar wanda daga bisani ya musanta labarin.

Har ya zuwa yanzu dai dan kwallon baice komai ba kan tabbacin wannan labari na sakin matar tashi.

0 Response to "News: Fitaccen Dan Wasan Kwallon Kafar Nan Wato Ahmad Musa Ya Saki Matar Sa"

Post a Comment