[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Uku

==>Aliya
tayi murnushi irin na wanda yadade yana begen abu yazo yasamu daga baya,tamike tsum tafice
kicin,kullum haka take saita kulla maganin inta kulla jakadiya na kallonta tana komawa sai tajuye
tahada wani, ahaka zuwa ran da tacika sati daya tadauko gyadan suya tana sane cewa yarima
abdullahi bayason waken suya,yakan kwantar dashi ciwo tasan hakane a binciken datayi tun
kafin isowanta fada,tasan matsalan kowa da kowa, donhaka acikin hadin alale tasaka garin waken suya ,aka kaimishi ,ta isa fannin falmata adaidai lokacin jakadiyar ta tashigo da gudu tana murmushi, ta sunkuya kanta akasa tace "gimbiya ga yarima abdullahi acan rai agurin Allah" falmata takalli aliya sannan tace "aikinki na kyau sosai dahaka zamu cigaba ciwo dai takamashi yanzu" mikewa tayi don kissa ta nufi sashen yarima abdullahi inda ake dubashi,tasamu yakolo na gun itama tayi tagumi duk tadamu, likitan yagama dune dubensa sannan yakalli yakolo wacce tamai alamu dayayi shiru karyafadi ko ma menene, falmata dasauri tace "meya sameshi? Dan masoyina?" Likitan yayi murmushi sannan yacev"zazzabi me kawai ba tsanani" falmata takalli idonsa tabbas tasan karya yake donhaka tayi murmushi sannan tace "toh Allah bashi lafiya
barin koma anjima zan dawo".

Fitanta tawuce fanninta anan ta kalli jakadiya tareda cewa " kema kingane karyane ko?" Jakadiya tace "ae wlh gimbiya boye miki sukeyi basuso kisani" falmata tayi dariya sannan tace "makirai
dukkanku saina kaiku kasa" Aliya na durkushe a gefe itadai kanta na kasa tana sauraren mesuke
fada, can jakadiya ta dan muskuta sannan tace "yazakiyi da wazirin toh?kinsan shiyake saka sarki yayi dole,abu kaman asiri,magananshi
kadai sarkin yakeji," falmata taja tsaki sannan tace "bar wawan mutum,gashi yanata janyo wa
mutane balai, mutane nawa wazirin yakashe anma kowa naganin laifin sarki, tundaga kan galadima hashim, har kan barade yusuf, " aliya wacce kanta ke kasa saida gabanta yayi mummunan fadi, owwh dama ba sarki bane ya
kashw babanta? Waziri ne? Lalle tana bukatan karin bayani kuma tasan jakadiya ce kadai zata
gaya mata donhaka ta nutsu dai har lokacin da falmata zata kwanta sannan suka fito suna tafiya jakadiya nagaba ita tana baya, sannan tace "ranki ya dade inada tambaya" jakadiya tace "mu isa
sashinmu tukum", sashin jakadiya da yanuwanta yafi na bayin dan fasalin gani da kyau,tana
durkushe akasa jakadiya tace inajinki, aliya ta numfasa sannan tace "bayanin kisan da waziri yakeyi, inaso kidan karamin bayani, inada masaniya akan yadda zaayi" jakadiyan ta kalleta sannan tace "bakida kai, kina baiwa mezaki
iyayiwa wazirin garinnan? Ko shi sarki ya yakare? Anma tunda kinason ji shikenan, akwai lokacin
da yafara hakan, yasamu saran kashe duk wanda yabata masa rai, hakan yasa sarki hada meeting akan zaa saukeshi abawa galadima
waziri tunda yafishi adalci da gaskiya, anma wazirin yayi hada hadansa yasa aka kashe galadiman, anzo zaa daura barade ma nan
yakara kashe barade toh kinga bawanda zaice mutuwa daga Allah kowa yasan akwsi dalili" aliya gabanta na tsananta fadi.

Tace "nagode insha Allah zannemo mana hanyan tsira" jakadiya dai jinta take don bata yardaba, ta
girgiza kai sannan tace "munajira" Fitan aliya fanninsu tanufa, lalle yakamata tabar fada duk tsanani saidai anya zaa barta? Baridai ta saci hanya, shigan kamala tayi kaman bakuwa ce tazo
tasami kayan agun bilki wacce tamata kashedi kala kala, sannan tafice gydanta tanufa tabude
dakinta har gurin yayi kura, wanka tafara shiga tagoge jikinta sosai sannan tanemi riga da skirt na atamfa yakamsta sosai,tayi sallah sannan tuni tajawo littafanta da abubuwan zane zanenta
tafara tunanin yadda zatayi da waziri toh ashe inhakane zaman fada baikamata ba, yakamata
tafice takashe waziri tukun, saidai baridai taga mezai faru, tana zaune har bacci me nauyi ya kwasheta tayi bacci sosai sannan tashinta
tacigaba da zane zanenta tayadda zata ci karo da waziri.

Gani tayi dare yayi bata damuba dama tariga data yiwa jakadiya bayanin zataje ganin
wata kakanta, inbaa gantaba, kuma ta amince bilki ce dai hankalinta yatashi sosai.l, karfe tara na dare zaman dakin ya isheta tuni tanemi dogon abaaya tasa sannan tafice tana tafiya tana danna
wayanta wani hotel ne wanda akwai restaurant aciki tunda tazo garin kafin ta isa fada agun
takecin abinci,shiganta tazauna tayi ordering indomie kawai,tanajira don saisun dafa kafin sukawo agefen gun taji hayaniya a hall mikewa
tayi tanufi gurin ga mamakinta ganin yarima yusuf tayi, wanda kwalban giya ne ahannunsa
babu dogari, gashi yafara layi aliya taja tsakibtareda cewa "useless" harzata tafi taga mutumin
dake aiki a hotel din yana jan yusuf akan yafice yusuf sai zuba hauka yakeyi yana surutai, abun yaci mata rai. Tanufi gun shi sannan tace "yarima yusuf ne don Allah kubarshi" mutumin baice
komi ba yatafi tajuya zata tafi yusuf yakamo hannunta ta mugun tsorata anma dai tadanne azatonta yaganeta ne, anma tunanin yana cikin maye hala ne inyaganen yaki saketa donhaka ta fizgeshi suka bar hotel din ,abincin da bataci ba
kenan, fitowansu tasakashi akan hanya takare masa kallo, asalin dolo ne, no wonder dan fari nebashe dole yayi wawanci tace cikin rashin kulawa da rashin damuwa " kawuce katafi gida, wani dolonci ne yasa kafito ba dogarai?yakalleta baice
komi ba can kawai yafara yunkurin amai, amai yakwara mata haushi taji kaman takamashi da duka.

Taja wani tsaki sannan tace saikayi ai , juyawa tayi tana tafiya harta isa kofan gidanta juyowan dazatayi taga mutum ashe biyota yayi babu yadda batayiba yaki,tashigar dashi tareda cewa "wlh ba yarima ba ko sarki kake inkamin amai anan duka zaka sha" saiyace "nifa dan sarki
ne kuma sarki!" Bata kulashiba ganin baya hayyacinsa toilet tashiga tacanja kayan jikinta
takara wani wankan sannan tace "kashige kayi wankan kaima, abun haushi bacci tasamu yafarayi wani salati tayi tareda cewa yau nashiga
uku!

Sourced By NovelTime.Tk

0 Response to "[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Uku"

Post a Comment