Halaccin Sarauta Kashi Na Shida
Aliya ta runtsa sannan tace "mekakeso dani?!" Cikin rashin
damuwa yace "kenake so" bata kalleshiba tadauko towel, tashiga toilet tajiko da ruwan sanyi, tana zuwa ta maka masa dasauri yace
"awhsh meye haka?" Fuska a murtuke tace "danna kace kana so!" Tana fada tana danna masa kafan lumshe ido yake cikin dadi don
shikam har ransa yadda yakejin sanyin haka yakeji aransa, sonta yake don jiya dakyar yayi bacci tun taimaka masa datayi take idda mishi gizo, mintsinansa tayi bashiri yabude ido, "meye haka?" Yadda yabata rai, saikace meshirin
kashe barawo, bata kulasa ba tamike tareda cewa "nagama" tajuya zata fita , samata kafa yayi
tuni ta tuntsire tayi kasa, cikin tausayi yace "wayyo kiyi hakuri " bata kulashiba tamike tafice, dadi
yaji aransa.
Itakuwa inbanda kwashe masa albarka ba abunda take a zuciyanta, fannin yakolo tanufa, jiki dasauki hamdallah, shima don sarkin yadauko malamai sukayi saukan qurani, sannan malamin yayita bayani " wannan adduan dakuke rainawa ance kunayi kunaga kaman
wasane,kuyi zikirin safe dana yamma ,Allah yana kareku, fatiha,falaq da nas , ayatul kursiy,ga
lailaha illa anta subhanaka inni quntum minal zalimin, lailaha illalahu wahdahu la sharika
lahu, lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shay in qadr, akwai su dayawa kunemi hisnul muslim shine makamin mumini, duk sharri da asiri da jinn Allah zai kareku, inhar kanayi kuma kaga wani abu yasameka toh kadauka wannan
kaddara ce kuma jarabawa, don annabi SAW anyi masa asiri kuma takamashi, anma kuma yakarya.
Don haka dole kuyi imani da kaddara, ku yarda Allah shiyake komi, babu yadda zaayi dan wani
abu yasameki saiki bude baki kice wacce ce tayimin haka, a a nikam anmin asiri, zato zunubi, Allah bayason haka, duk abinda yasamu
mumini anaso kayi imani kakuma fuskanceshi, zama kace anmaka asiri kana biye biye ba daidai bane,
safe da yamma ko yaushe ka kasance da adduanka," yakalli jakadiya tare dacewa "abasa qur'an"
tamika masa yakalli qur'anin gashinan dai anma sai kura alamun cewa andade ba a budeba, yace
"toh kunga wani matsalan meye amfanin fansar quranin da zaa ajiye don ado?,ba gwara kubayar sadaqa a masallatai ba?,sai kuga agyda ansiya qur'an sama da goma, an ajiye wato acemuku musulmai kuba arna bane, ina amfanin haka baka karanta qurani, anma kullum zaa kunna tv, zaa hau whatsapp, facebook, wata inbatahau ba
kaman zatayi zazzabi, zaatashi tsakar dare ayita waya kuma sai akwanta goshin asuba, anmanta
da Allah waiyazubillah, yakamata duk mu tsarkake ranmu, bature yazo mana dawani cuta mai wuyan magani,duk wannan social media
din cutane, Allah ya tsaremu, yakuma kara mana imani, anma dole mucanja inhar munaso muga
mai kyau, rashin bin Allah da dokiknsa shike sawa muke ganin jarabawa kala kala, " duk kowa jikinsa yayi sanyi sarki kansa yaji
wannan waazin don yamanta wen last yabude qurani, gwara sallah yanayi dukka a masallaci anma
baya farilla, falmata kuwa wacce tazo daga baya , bindin shedan tamanta wen last tayi sallah,
donkuwa a maganin da akabata an umurceta da kartayi sallah na kwana arbain, donhaka take
zuane, yakolo kuwa baiwar Allah wacce tayi imanin jarabawa take fuskanta agun ubangiji taji
dadin jawabin malam ko ba komi zai kara mata tuni da mutuwa dakuma kwanciyan kabari, bayan anwatse aliya tanufi dakinsu tasamu bilki wacce ita tana kwance tana hutawa tamike tareda cemata "matan sarakuna yaushe zasu
kara zuwa?"
Bilki tace "ran laraba
menene?"aliya tace " babu kawai inason sanine" dadi taji ganin plans dinta yana tafiya daidai, Ran
laraba dasafe tanufi gun dogari isa, shine wanda tasaba dashi sosai kuma tarokeshi alfarmar yanema mata kayan dogorai set daya, duk da yaso yakawo mata taurin kai.
Dubi goman ta mint tahada
tabashi,ba bata lokaci ya amince, donhaka ta karba tanufi baya tasaka tarufe kanta, tadauko fatar gemu wanda tayo guziurin kayanta tun
daga kudu, tsayawa tayi a babban gate gurin da dole kayan sarakunnan sushigo, a tsayawanta
tafara gadi, dogari isa ne agefenta abun mamaki dukka dogaran bawanda yace komi asalima
basu nuna sunsan bakon fuska bane, hakan yatabbatar mata dacewa dogari isa yatoshe bakinsu, oh kudi samunka mutunci, rashinka
balai, karfe daya daidai suka iso, matan sun shige yayinda kayansu dole aduba kamar yadda sarki
ya umurta, ahaka aliya tagama cuse cusenta takulla komi sannan tacire kaya tabawa dogari isa, wanda tuni ya ajiye a boyeyyen gu don kar
asiri yatonu, anshiga anyi iso ma matan sarautan harda mazajen nasu, lami lafiya anci abinci
anyi tadi, anan aka fara fitar da kayan kowa ana dubawa, matan sarkin sun nua farincikinsu
musammamn ma yakolo wanda don ita akadawo dazuwan laraba musababbin ciwonta, sarkoki
ne, sai laces,shadoddi. Da kayan kwalama, can kasan wani shadda gezner jakadiya tana budewa
sai ga laya da zobe, gaba daya hankalinsu yayi kan gun don sun mugun tsorata , jakadiya wacce ada take gudan farin ciki tana kirari
saigashi tafara salati, tuni hankalim kowa yayi gun, umma uwar soro ce tanufi gun tareda cewa "kayan
waye" jakadiya tace "na matan waziri" falmata wacce ta harzuka sosai tace "ku kamata" bashiri
dogaran suka nufo kanta tareda bata hanyan fita, magana kaman iska tuni fada tadauki hayaniya
waziri wanda ke fadar sarki jin abunda yafaru yasashi rudewa, bashiri ya roki da abarshi yashiga daga ciki, anma sarki yace mai " uwar soro zata mata hukuncin daya dace, babu ruwan fada ko sarki aciki".
Falmata kuwa abunnema
yasamu duka sosai matar waziri eshallo tasha, Yakolo bataji
dadiba acewarta yakamata ko darajan sarautan mijinta a lamunta mata, anma falmata taki , dadi takeji
tasamu naman fansa akai, bakin ciki kaman zai kashe waziri anma babu yadda ya iya, uwar gayyan kuwa aliya taji dadi acewarta yanzu
tafara daukan fansa, tunda yarabata da kowa nata saita rabashi dakowa nashi da duk wani wanda yasa
hannu a kashe iyayenta, tana zaune bilki tashigo tareda cewa kizo inji yarima yusuf, shiganta tasameshi yana zaune da kwalban giyansa, da
alamun maye, tuni tadaure fuska, yakalleta tare dacewa "kinga ko ni yarima ne, kuma kome nakeso ina samu, ina sonki kinji? "Aliya bata
furta komi ba, kwace kwalban tayi tareda ajiyewa agefe.
Kallonsa take sosai, yusuf namiji iya
namiji saidai yasaka shaye shaye agabansa duk yayi baki yadawo wani iri, wannan wani irin rayuwa
ne, itama zata iya amincewa kanta cewa tana sonsa saidai soyayya yanzu bashine solution dinba, gwara tadanne ranta tabi hakkinta tukunna, tajuya zata fice taji yana sumbatu, kwance akan kujera, zuwa tayi tagyra masa kwanciyan tadauko bargo tarufesa sannan
tazura mishi ido gashin girarsa acike yake ga gashin akwance tamike zata fita taji yaruko hannunta, Kufara turowa adda bena da naman sallahnta.....
0 Response to "[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Shida"
Post a Comment