An fitar da jerin sunayen 'yan wasa da fina-finan da za su iya samun lambar yabo ta Kannywood.
'Yan wasa ukun da aka ware don bai wa daya daga cikinsu Gwarzon Dan Wasa a bana su ne Sadiq Sani Sadiq saboda hazakar da ya nuna a fim din "Bayan Duhu" da Adam A. Zango saboda rawar da ya taka a "Gwaska" da kuma Ali Nuhu saboda basirar da ya nuna a "Nasibi".
A bangaren kyautar Fitacciyar 'Yar Wasa kuma, wadanda aka zabo su ne Jamila Umar, wacce aka fi sani da Jamila Nagudu saboda ficen da ta yi a "Na Hauwa" da Rahama Sadau "Halalci" da kuma Nafisa Abdullahi "Baiwar Allah".
Sauran wadanda aka bayar da sunayensu da suka cancanci samun kyauta su ne:
Dan Wasa Mai Rufa Baya: Lawan Ahmad "Da'iman", Sadik Ahmad "Nasibi", Ali Nuhu "Rumfar Shehu".
'Yar Wasa Mai Rufa Baya: Ladidi Fagge "Da'iman", Fati Shu'uma "Basma", Fati Washa "Hindu".
Sourced By BBC Hausa
0 Response to "[Kannywood] An Fitarda Jarumai Uku Daga Cikin Maza Da Mata Wadanda Zasu Iya Zamowa na daya a Wannan Shekara"
Post a Comment