[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Biyu

==>Tazauna tana nazarin fadan da yadda komi take, takalli bilki sannan tace "inane hanyar fadar sarki?" Bilki tajata tareda cewa "zomuje" kaf saidata nuna mata hanyan fannin kowa tundaga kan sarkin isa, zuwa ga matansa gimbiya falmata da gimbiya yakolo, tace "sauran matansa biyun gimbiya ainau da gimbiya atika sun rasu kwarkwaransa sunkai hudu wanda ni kaina bansan sunayensu ba,umma uwar soro itace tasan kome dake cikin fada ta fannin mata, Aliya
tace "toh fannin yara fa? Bilki tace "yaran sarki su sha takwas ne, bakwai suna karatu akasan waje,
sauran suna zaune anan,suma don su sukaki tafiya,anan munada yarima yusuf,yarima abdullahi,yarima shehu,sai fulani hauwa, fulani hafsat, fulani zainab, sauran kananun yarane, ihsan,isham,ilham,ashfaq,,ashraf, manyan daga kan abdullahi, yusuf shehu,zainab ,hauwa hafsat,kowanne nada bayinsa dakuma fanninsa.

Kananun ma sunada fanninsu agefen na iyayensu, in batun hali ne kuma yarima abdullahi shine ya gado halin ubansa na dattako, yarima yusuf yanada wulakanci bar ganin yau yamana shiru gobe zai iya watsa mana wulakanci, amata
kuma zainab itace ta kirki saidai tacika fada, hafsat da hauwa kuwa girman kai, a tsakaninsu ma rikici suke, saboda iyayensu daban ne, da
hafsat, zainab da yusuf , ilham , ashfat uwarsu daya wato falmata, yayinda abdullahi, shehu, hauwa,ashfaq,ihsan,isham uwarsu daya, wato yakolo, sauran na kasan wajen yayan atika, da ainau ne bansan sunayensu ba dai, anma babban
dan sarkin shine yusuf, sai abdullahi, sai wani akasan wajen Tana bayaninta aliya tana kallonta
can tacigaba dacewa kuma kinga anan falmata da yayanta su suke mulki donhaka kinsan kowa
yafi bin inda akwai tsoka nafi ladabi wa yan dakin falmata kuma nafi samu" aliya tace "anma ai kinashan wulakanci" bilki tace wannan dole
musha.

Haka sukayi ta tadi har dare sannan suka koma kai abinci sunsameshi zaune yana waya suka jera abincin akan table sannan suka ja suka
tsaya, aliya najinshi ya idar da wayansa tsaf sannan yataho kan dinning din bude abincin yayi
cikin rashin damuwa yanuna aliya "ke zonan!" Ta matso ahankali kanta akasa daukan abincin yayi
ya watsa mata!, saiga miyan egusi.

Wanda yasha kamshi tas ajikin aliya, bata dago kanta ba bata
kuma furta komi ba, bilki ce dasauri tanufo gun ta sunkuyar dakanta akasa tana bashi hakuri itama
daukan sakwaran yayi ya watsa mata, sannan yaja tsaki yabar musu gun, abinda aliya ta tsana arayuwarta wulakanci, lalle yanaso taci kaniyanshi, baya cikin lissafinta anma karya bari tasashi aciki don zaiga ba daidai ba, daukan tray
din tayi tafice, bilki kuma ta tsaya bada hakuri, cikin zafin rai yace takoma takira aliya, shi acewarsa akan me zata tafi bazata rokeshi
ba,akan me bazatayi ladabi agareshiba,bilki dasauri tashigo dakin inda tasami aliya tacanja
uniform tasaka wani, dankwalin kanta take daurawa,tace "yarima yana nemanki meyasa zaki
tafi baki bashi hakuri ba?"

Aliya cikin rashin damuwa tace "saboda bazan tsaya jikina a bace
agunba" toh dai kizo muje kibashi hakuri" aliya tayi shiru tabita suka koma wanda yana zaune akan laussasan kujerarsa yahade kafa daya kan daya, gashin kansa ya kwanta luf luf sunkuyar dakai sukayi akasa, bilki tafara bada hakuri anma
aliya bakinta tsit" bilki tafara tunkude aliya domin itama tayi magana anma aliya kam taki cewa komi, can dai yace "ke dago kanki naganki"aliya bata dago ba bashiri bilki taja kanta wanda saida
dankwalinta yafadi akasa gashin kanta yaxubo yarufo mata kai, cikin rashin damuwa yakalli bilki
tareda cewa "aina kuka samo wannan bakan?

Kije ki aske mata gashi banison ganin gashi, balle yazubemin a abinci, aliya wani murmushi tayi
wanda itakanta sai Allah sukadai sukasan meke ranta, ni kaina benaxir na tausaya mashi sosai,ficewa sukayi bilki jikinta na bari, suna shiga dakin tace don Allah yazamuyi?" Aliya tacire kanta tareda cewa "aske zuwa yanda yakeso"bilki taji.

Hauahi har ranta anma babu
yadda ta iya tarage gashin aliya yadawo dan daidai yanda sauran nasu yake, sannan suka
zauna, bilki tayi mamakin ganin aliya bata damuba,anma aliya tace mata "ke indai gashin kainane kibashi sati biyu zakiga yadda zai dawo" tadai bari aranta dahaka suka kwanta bacci, washegari dassasafe suka nufi fannin sa yana
bacci donhaka saida suka jirashi ya idda baccinsa,sannan suka shiga yayi wanka abincinsa suka basa, sannan suka hau gyran dakin, suka share sukayi goge goge sannan suka gyra mishi lallausan gadonsa dakin tuni yagume da kamshi alokacin harya fice da dogaransa, sunfito kenan aliya rike da roban
dasukayi goge goge kanta akasa tanadan sauri, sai jitayi tabugi mutum, tuni wani dogari yayo
kanta zai maka mata sandanshi anma cikin zafin murya taji ance "rabu da ita" bai juyo yakalleta ba
yaci gaba da tafiyansa bilki cikin tsoro tace "waike meye matsalanki? Yarima abdullahi nefa wannan kinci saa ba yayan bane da yau saikinyi
tsallen kwado" aliya taja numfashi tabi yadda yabi dakallo sannan suka fice, Umma uwar soro ce tabukaci dukkan bayi masu aiki dasu hallara
wanda aliya tashiga cikinsu tana sauraro, cikin izza tace " munsamu labarin akwai wanda basa aikinsu dakyau, yau yarima yusuf yamin bayani akan yanason canjin masu masa aiki, donhaka kuzo kudauki hukuncinku kafin naci gaba da magana bilki da aliya ne suka fita inda suka mike akabasu bulala hamsin hamsin, gwara bilki
tasaba anma aliya tunda uwarta ta haifeta zunguri bata taba sha mai lafiya ba, nan da nan jikinta ya kumbura fatanta yattatashi, dakyar
akayi daki da ita, zazzabi ne mai zafi yarufeta wanda saida umma tanufota tareda cewa duka hamsin kacal shine kike mana ciwo? Kimike
yanzu a kicin zakina aiki, agun zaki dauwama, bilki har hawaye tayiwa aliya anma babu yadda ta iya , aranar saida aliya tanufi kicin yadda taga girman tukwanen saida cikinta yakada saura kadan ta tsure, wasu manyan tukane ne. Dasu ake girkin gydan, ga kicin din uban zafi, haka dai aliya tadaure, iyakacinta kicin sushiga dasafe sushiga darana suzo kuma sushiga daredare ciwon baya da ciwon jiki yasaka aliya takar ramewa, takara dawowa baka, idonta yakara fitowa, tuntana shan wahala har tasaba, Watarana tana zaune a kicin babu tunanin da
batayiba, yakamata tabar kicin dinnan takoma wani gu daban inbahakaba zuwanta yazama na
banza, jakadiyan gimbiya falmata ce tanufo kicin din bashiri kowa yamike yanuna ladabinsa, tabi su daya bayan daya sannan ta je wa aliya "kizonan" aliya tabita basu nufi ko ina ba sai fannin falmata.

Macece wacce bata wuci arbain
ba,fara ce kyakyawa saidai daga kallonta kasan ba karamar makira bace,cikin kissa ,kissisina da
izza take rayuwanta, zuwan aliya yasa takalleta sama da kasa sannan tacewa jakadiya wannan
kika samo? Jakadiya tace "itace tayi saura a masu ilmin bayin" falmata takalli aliya sannan tace "da
alamu kingaji da kicin din?" Aliya wacce ta durkusa kanta akasa tace "ae ranki shi dade" falmata tace "zan aikeki karki bude aikan inkinkai lafiya toh zaki dawo gefena da aiki" aliya tace "komi kikace ranki shidade" jakadiya ce tamika mata takarda tareda cewa" zaki kaiwa
umma uwar soro" takarbi takardan sannan tafice harta kusa isa zuciyanta yaraya mata data bude
takaranta budewanta taga anrubuta "ki kasheta" abun ya tsorata aliya, metayi wa gimbiya?

Babu! Toh gimbiya na gwadata ne duk yadda akayi, tunda taji tace "itace tayi saura a masu ilmin bayin" gwajine! Donhaka ta nannade takardan tanufi gun umma uwr soro wacce tabude takaranta cikin izza tamike ranta abace tace kinsan mekika kawomin kuwa?

Kinfa kawomin cewa za'aje akashe gimbiya falmata ne, aliya aranta tace "bahaka bane tabbas gwajine" waya baki ?

" babu bansan wayeba" babu yadda umma batayiba har kiran dogarai tayi suka dirke aliya taji jiki sosai anma taki magana, candai saiga jakadiya tazo takarbeta fannin falmata takaita, falmata tayi murmushi sannan tace "kinwuce
gwaji" donhaka na amince dake zan ci gaba da aiki dake, zakibar kicin kidawo fannina, sannan ungo wannan tamika mata wani kullin magani, inaso kije kisaka a abincin da zaakai fannin abdullahi naji labarin ke kike zubawa"aliya tace
"komi kikeso rabki shidade shizanyi" dahaka tamike tafice dakinsu tanufa tana tunani, lalle makirci da duk wani kissa da izza yakare a maitan
son mulki wato tasan danta yusuf baida hankali tunda shaye shaye yake bazaa bashi mulkin garinba gwara takashe abdullahi ahankali sai shehu, oh Allah, dahaka har yamma tayi tafita da kullin jakadiya nabiye da ita tana leka ta, ahadin
abincin yamballs ne saita zuba, tana zubawa jakadiya tafice, bashiri taxubar da wannan kwabin sannan takarayin wani, tashirya tsaf aka kaimishi, sannan tanufi fannin falmata tana durkushe kanta akasa sannan tace "na zubo ranki shi dade" falmata tayi murmushi sannan tace "kullum zakina sakamishi, maganin tsotse
jinine, zaisamishi karamin hauka, kinga idan yahaukace bawanda zai karbi mahaukacin sarki gwara dan shaye shaye," aliya tayi murmushi
sannan tace " gidan shikenan har abada yazama naki gimbiya, mata mai ran karfe, wanda yatabaki
yataba zakanyan jeji mai cutar hauka, sai ke mata kadai azuciyan sarki, daga mulkinki babu
nakowa yayinki bamai karewa bane, takawa lafiya gimbiyan sarki, uwar sarki kakan sarki," falmata takalleta sannan tace "kkigama aikin ki
na kicin daganan kindawonan da aiki yar gari!"

Sai Mun Hadu A Kashi Na Uku Kuma

Sourced By NovelTime.Tk

1 Response to "[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Biyu"

  1. Muna jin dadinku kam
    Sannan kuma don Allah in kuna da group wanda kuke turo littafan hausa a whatsapp sai a sanyamu ciki da wannan lamban 08137371414

    ReplyDelete