Jarumar Shirin Hadiza Gabon za ta je Amurka, ita da wasu masu shiri da kuma ba da umarni a fina-finan Hausa a Najeriya.
Cikin jaruman da za a yi tafiyar da su, sun hada da Ali Nuhu da kuma Hauwa Maina.
A cikin masu shiryawa da bayar da umarni kuwa, da akwai Hafizu Bello da Kamal Sani Alkali, da Nazifi Asnanic da Bello Mohammed Bello, da kuma Hassan Giggs.
'Yan Kannywood din za su halarci wani taron karawa-juna-sani na makonnin biyu ne, a wata makarantar koyar da dabarun shirin fim da ke katafaren cibiyar shirin fim ta LA Studios Center.
A yayin ziyarar, za su ga yadda ake shirya fim na zamani, za kuma su koyi sabbin dabaru na shirin fim wanda zai taimakawa fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.
A hirar da BBC ta yi da Mohammed Sani, na kamfanin da ya shirya tafiyar ya ce, ziyarar hadin gwiwa ce da wani kamfani mai son taimakawa shirin fina-finai a Najeriya, musammnan wadanda ake yi da Hausa, saboda tasirinsu da kuma karbuwarsu a duniya.
A ranar Talata 9 ga watan Fabarairu ne jaruman za su tashi zuwa Amurkan.
Wannan ziyara ta zo ne a lokacin da ake shirin bikin bayar da kyatuttuka na Kannywood Awards a watan Maris, da kuma bikin cika shekaru 25 da soma fina-finan Hausa a Najeriya.
0 Response to "[Kannywood] Jarumar Shirin Film Din Hausa Wato Hadiza Gabon Zataje America"
Post a Comment