Masana'antar Kannywood Zata Fara Shirya Fina Finai Masu Dogon Zango

Kamar yadda daya daga cikin fitattun marubutan Finan Finan Hausa na Kannywood industry, kuma jami'i a hukumar Moppan, Balarabe Murtala Baharu,  a cikin wata tattaunawa da yayi da gidan Jaridar  Dandalinvoa dake yanar gizo ya bayyana.

Gadai Yadda Tattaunawar Tasu Ta Kasance
A shirinmu na nishadi a wannan mako na mussaman ne, domin kuwa mun samu bakonci Balarabe Murtala Baharu, marubucin fina-finai da shirya fim a Kannywood industry, kuma jami'i a kungiyar shirya fina-finan ta Moppan.

Mun zanta da shi ne akan sabuwar dabi’ar da wasu manyan kamfanoni, dake shirya fina-finan suka fi maida hankali kan shirya fim na gidajen talabijin, madadin yin fina finai da aka saba da su na kamar awowi daya zuwa biyu.

Ya ce wannan sabuwar hanyar, ita kasashen da suka cigaba ke amfani da, wajen samun riba mai yawa, tare da lokacin mai yawa don bada labari gamsashe.
Ya ce sanya fina-finan a talabiji ya fi bada damar fidda labari, yadda ya kamata, sannan kasuwancin duniyayta koma kan yanar gizo.

Baharu ya ce, satar fasaha na daya daga cikin manyan dalilan, da ya sa wadannan kamfanoni suka canza sheka, da bin sahun kasashen duniya.

Source - Dandalinvoa

0 Response to "Masana'antar Kannywood Zata Fara Shirya Fina Finai Masu Dogon Zango "

Post a Comment