Kannywood: Jaruma Halima Atete Ta Bayyana Dalilin Dayasa Taki Aske Gashin Kanta

    Halima Atete tana daga jerin jarumai mata wanda duk irin matsayin da kace su fito zata iya fitowa. Tana fitowa amatsayin masifaffiya misali cikin fim din “Dakin Amarya” sannan tana fitowa amatsayin mai barkwanci misali cikin fim din ” Mata Maza” tana fitowa matsayin soja misali cikin fim din “Auren Soja”. To abinda yaba sauran daraktoci mamaki shine kin yarda da ta fito cikin wani sabon fim na mawaki Nura M Inuwa maisuna “SULTANA”. Jarumar ta fadi dalilan da suka hana ta fitowa acikin fim din Sultana. Acewarta:
    .
    Ni dai bazan iya fitowa amatsayin jarumar cikin fim din ” Sultana” ba. Sabida dalilai masu tarin yawa. Dalili na farko shine labarin fim din ya nuna cewa dole sai an aske gashin duk jarumar da zata fito acikin fim din. Ni kuma gaskiya bazan yarda da haka ba. Domin ya sabawa addinin Islama kuma Allah ya tsinewa duk macen da ta aikata haka.
    .
    Na biyu, na tambayi iyayena shawara akan haka amma sunce idan na aikata haka to tabbas tsinuwar Allah da tasu zata tabbata akaina. Ni kuma duk abinda iyayena sukace kada nayi to Wallahi ko nawa zan samu bazan yi shi ba. Ko wannan fim da nakeyi sai da suka amince sannan na fara yi.
    .
    Na uku, gani nayi mutuncin mace da kwarjina shine kamin kanta. Idan na aske gashin kaina to zan sami kudi amma kuma zan rasa mutuncina a idanun duniya. Masoyana ba zasu yi farin ciki ba idan na aske gashin kaina.
    .
    Na hudu, samarina zan daina burgesu da dogayen gashin kaina. Duk da nasan wani gashin zai fito amma kafin ya fito nasha bakin ciki mara iyaka.
    .
    Sannan ni bance Nafisa da ta fito acikin fim din Sultana ta aikata laifi ba. Ra’ayinta ne yasa ta fito, ni kuma maganar Allah ce ta hana ni na fito, amatsayin wadda za’a askewa gashin kanta.
Rubutawa:=
Adamu Sani Chiroma

0 Response to "Kannywood: Jaruma Halima Atete Ta Bayyana Dalilin Dayasa Taki Aske Gashin Kanta "

Post a Comment