[Kannywood] Farashin Jarumi Adam A Zango ya koma naira miliyan daya a duk Fim din da zai fito.

Jarumi Adam A. Zango Ya Kara
Farashinsa Da Yake Karba a fim daga Naira Dubu Dari Shida (N600,000.00) Zuwa Naira Miliyan Daya
(N1,000,000.00) a kowane fim da zai fito daga kashi na Daya zuwa kashi na hudu (1 to 4), haka kuma duk fim
din da zai fito a ciki indai kashi na daya zuwa biyu ne (1 and 2) zai amshi naira Dubu dari Biyar (N500,000.00).

Wai Jarumin yayi wannan karin ne
domin ya samu hutu kuma a kara samun Bulbulowar Sabbin Fuska.

Indai Baku manta ba a watan Augusta na shekarar da ta gabata ne 2015., jarumin ya fitar da Wata sanarwa
makamanciyar irin wannan Inda yayi ikirarin cewa duk
Fim din da kasafin kudinsa bai kai miliyan biyu ba kada ma a tunkaresa dashi. Tun a wancan lokacin maganar tasa ta jawo cece kuce a masana'anatar kannywood,
inda wasu 'Yan Fim din suka goyi bayansa akan haka.

wasu kuma suna ganin wani nau'ine na girman kai ya Dora wa kansa.. Fittaccen Jarumin dai ana ganin shine
Dan Fim din aka San farashinsa tun kafin ka gayyatoshi aiki.


0 Response to "[Kannywood] Farashin Jarumi Adam A Zango ya koma naira miliyan daya a duk Fim din da zai fito."

Post a Comment