INTRO
Mata iyayen giji mu fito mu dafa masu,
Sun zama abin tausayi a kasa mu kama masu,
Mata iyayen giji mu fito mu dafa masu,
Sun zama abin tausayi a kasa mu kama masu,
VERSE 2
Maza a bawa mata yancin su roko muke,
Maza a basu dama su sake kamar mu suke,
Mu daina raina mata da yawan mu shirme muke,
Gurin mukamai a bawa mata suma su rike,
Fagen siyasa asasu ciki dabaru muke,
Duk namijin dake dukan mace shirme yake,
Duk macen dake dukan namiji shirme take,
CHORUS,
Mata iyayen giji a fito a dafa masu,
VERSE 2
Waka na shirya akan mata nakeyi musu,
Mata iyayen giji,
Mata iyayen mune su karmu bata musu,
A fito a kama musu,
Ladabi biyayya masoyana mu dingayyi musu,
Mata iyayen giji,
Murya ta canji tazo purple a sara musu,
A fito a kama musu,
Mace ko ina na da yanci kar mu tauye musu,
Mata iyayen giji,
Kuma nada hakki akan mu mu daina dannemusu,
A fito a kama musu,
Ilimi ginin rayuwa mata mu koya musu,
Mata iyayen giji,
Kuma ko suje suyi karatu mu dafa musu,
A fito a kama musu,
Mata da damar su kar mu sake ta kwace musu,
mata iyayen giji,
CHORUS,
Mata iyayen giji a fito a dafa masu,
VERSE 3
Buga tambari baitikan danake da mata nake,
Mata iyayen giji,
Dan naga yau rayuwar su cikin kazanta take,
A fito a kama musu,
Wasu ga mazan babu tausayi sai jigata suke,
Mata iyayen giji,
Wasu gasu sun yo karatu ba abun da suke,
A fito a kama musu,
Balle ace mai gidan su cikin talauci yake,
Mata iyayen giji,
Inya zo miji babu mata babu, rigima ake,
A fito a kama musu,
Kaga rayuwa babu ci ba sha, da muni take,
Mata iyayen giji,
Kafin akai matsayin rabuwa dabara ake,
A fito a kama musu,
Maza samu aiki ka bata rufin asiri yake, mata
iyayen giji,
CHORUS,
Mata iyayen giji a fito a dafa masu,
VERSE 4
Da abunda kalubale zaisa na daina muku,
Mata iyayen giji,
Yancin ku ya zama dole na dinga kare muku,
A fito a kama musu,
Hakkin ku banso na ganshi anata tauye muku,
Mata iyayen giji,
Damar ku inta fito a fito a damka muku,
A fito a kama musu,
In ci gabar rayuwar ku tazo a fito a mika muku,
Mata iyayen giji,
Lamarin siyasa ina mata na shaida muku,
A fito a kama musu,
Da ku ciki har mukamai zaa damka muku,
Mata iyayen giji,
In kunka ja baya ba abunda za ayi muku,
A fito a kama musu,
Kuma babu komai da za ayi dan faranta muku,
mata iyayen giji,
CHORUS,
Mata iyayen giji a fito a dafa masu,
VERSE 5
Mata abun tausayi ne zamanin nan nace,
Mata iyayen giji,
Kuma gashi sunyo karatu babu aiki nace,
A fito a kama musu,
Gashi mai gida babu aiki babu jari nace,
Mata iyayen giji,
Daga safiya yayi yai wakan sa sai ya fice,
A fito a kama musu,
Kye zaa kyale da yara ba sukuni nace,
Mata iyayen giji,
Wani ko yana nan a kwance gida kamar sankace,
A fito a kama musu,
Daga ka fito ka gaya masa gaskiya zai fice,
Mata iyayen giji,
Wani ma idan ka matsa masa saiki dauko ice,
CHORUS,
Mata iyayen giji a fito a dafa masu,
VERSE 6
Sakon purple ne suke Ali ni bazawa nake,
Mata iyayen giji lallai da girma suke,
Purple tace acanza lamarin da girma take,
Mata abar hantara wasu har da duka suke,
Purple tayo bincike ta gane illa ake,
A bawa mata hakki har shugabanci suke,
Purple tace a duba mata da tausayi suke,
Balle fagen amana mata rukewa suke,
Purple tace a mike ilimi da dadi yake,
Purple tace a canza mata da kima suke,
Sakonkune matasa kuma bayani nake,
A kula a bawa matasa hakki suma dasu yau ake,
Dasu yau muke,
Kuma dasu yau kuke.
0 Response to "[Music+Lyrics] Ali Jita Mata Iyayen Giji"
Post a Comment