[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Bakwai

cikin numfashi yace ina zakije? Aibanyi baccinba" tadan musguna gefe sannan tace "toh meruwana?" Ficewarta tayi gabanta nafadi daki
tanufa ta kwanta tana tunani, alokacin bilki tashigo take mawa aliya bayanin cewa dakyar
waziri yaroki alfarma yanzu dai anrufe matarsa harsai ran asabar ayi hukunci, bayan aliya ta idar
da sallahn isha tanufi fannin yakolo wacce tasamu sauki kaman ba ita bace a kwance kwanaki, abdullahi na gefenta suna magana koda aliya ta tambayeta ko akwai abinda take
bukata tace babu tafito kenan tana tafiya taji ankirata "baiwar Allah" tajuyo tareda sunkuyawa yamika mata glass hannunsa alamun takarba, tamika hannu zata karba sai yafado shiyasake itakuma bata karba ba, tuni ta sunkuya tafara
kwashewa jikinta na bari karya mata wani abu,sunkuyawa shima yayi yafara kwashewa ,jikin kwalban ne yadan shiga yatsanta, wani kara
tasaka, tuni yariko hannun yana dubawa yayi mamaki kwarai dayaji hannunta da balain laushi, don asaninsa bayi dai kam adan wahalan dasukesha jikinsu tauri gareshi kaman ma icce, cire kwalban yayi wanda saidatayi dan kara.

Hakan yakara bashi mamaki domin wannan dan ciwon bawani abu bane inhar cikakkiyar baiwa ce, yanaso yatambayeta tarihinta tun farkon
xuwa gydan yake mata kama da yasanta awani guri anma yarasa ainane, mikewa tayi tareda bashi hakuri yace bakomi, anan tasaka kai
zata wuce fanninsu ga mamakinta saitaga yusuf a tsaye kaman tsohon zakanya daya fi shekara baici abinci ba, batace komiba tawuceshi shima
komawa yayi, dama asali gunta zaije saikuma yaci karo da ita tare da kaninsa, wanda bayaso, lallaima yarinyannan zataga tsiya, ranan baiyi bacciba yanata tunani kodai soyayya suke?
Yanzi hakahala ya rungumeta kafin yazo? Toh meye suka rike hannun juna? Kanshi ne zata fara ciwo
tuni yajawo giyansa ya kwankwada sannan yacigaba da hidimarsa domin kuwa ya manta shagaf da bakin cikinsa, Bilkisu ce tafarka
tsakar dare saikuwa taga aliya akan salllaya tace "kekam kullum ne saikinyi sallahn nan? kowacce
dare inna farka saina ganki akan sallaya baccin awa nawa kike? Gashi bakya baccin rana sai jifa
jifa," aliya tayi shiru sannan tace "akullum dan adam mai neman biyan bukata ne, akullum yakan so wani abu, koda wannan bukatar
tabiyu toh zai samu wata tafito. Don haka meyesa bazan juya alkiblata agun mai amsa adduoi ba? Mai
Jinkai? Mai Buwayi? Mai Girma? komi shine, duk wanda yarike Allah da manzonsa bazai taba wulakanta ba, bazaiga wulakancin duniyaba,
duk kuma mai sallahn dare akwai wani haske da yakesamu agun Allah, akwai daukaka da daraja
da Allah yake basa a idon duniya, yana hani da mummunan aiki, donhaka ni inada bukatu na
Allah yakareni, yajikan iyayena yakuma biyamin bukatata don nacimma burina kema dakin fara
haka bazaki taba tozartaba!" Bilki tayi tunani sosai maganan aliya gaskiya ne bata taba shiga
wani tashin hankalin dazaa wulakantataba, asalima tafi shekara 10 agydan anma aliya datazo
a watanni kadan tafita farinjini, kwarjini, kima da mutunci agun mutanen gydan har masu aikin
gydan, gaskiya dole tafara itama dahaka tamike tayo alwala itama tafara sallahn,gari na wayewa
aliya tanufi fannin falmata wacce ta watsake sosai tadanyi aikacen da bazaa rasaba, sannan tafito
ahanyarta taga abdullahi yana ganinta yafara murmushi "yakike? Ya hannunki?" Ta amsa da
" lafiya lao" yayi mumushi sannan yawuce,isanta dakin ta tarar da bilki tana jiranta , tace ina kuma
zamuje?" Bilki tace "gun yarima yusuf don yin aiki" tamike akan gado takwanta tareda cewa
"atunannina niba baiwar sa bane yanzu, a fannin gimbiya nake" bilki arude tace "anma dai kinsan
inbanje dakeba wulakanci zansha ko? Don Allah kiyi hakuri muje!" Aliya ganin bilki zatafara mata
kuka tamike suka nufi fanninsa, yana kwance yaki tashi jin muryan bilki ya daka mata tsawa tareda cewa tafice tabashi gu!" Aliya ce tace "kayi hakuri yarima" shiru yayi hakan yabata daman bude kofan suka shiga, tuni suka kimtsa gun,
yanakan gado bai motsaba, sukayi sharansu da goge goge, sungama alokacin yamike bilki tadauko abincinsa, ta ajiye, harsun fice suna
tsaye suna jira yasauko daga kan gadon tareda nuni ma bilko na tafita, ficewa tayi aliya bataji dadiba
anma babu yadda ta iya, tazuba mishi yaci duk shi kallonta yake sosai, yaki yakyafta ido yadda
take servn dakomi yabashi mamaki, cikakken wayayyiyar macece tasan yadda ake handling fork, da yadda ake servn duk da cewa bayin gydan anyi training dinsu na alada anma yadda aliya take nata dabanne, ganin kallon yayi yawa ta tashi takoma inda suke tsayuwa tana jira
yagama, , yagama ci a nutse sannan tazo kwashewa cewa yayi tazauna, hankali akwance tazauna abunta, shikam tana bashi mamaki irin
tsoron da bayi mata suke if aka musu haka saboda ana sani koransu ake, anma aliya hankalinta akwance yace "zan iya jura idan
kikace baki sona, anma bazan iya jura naga kina soyayya dawaniba, yafi ciwo!" Takaleshi fuskarshi asalin alaman tausayi ne, kana
ganinsa kaga wanda ya tsume a soyyayya, abun tausayi
duk fadin ransa da mulkinsa ji yadda yake ladab agaban mace, nimadai benaxir abun yaban
mamaki, aliya tace "nifa karka jawomin akoreni, banda hanyan ci da sha sai agydannan,!" Wani
kallo daya saka mata sai datayi shiru, yace "kigayamin waye ke ko inyi maganinki bakiyi kama da talaka ba, babu komi naki mai kama
da talaka , takalli jikinta sannan tace meka gani ajikina, ko dankunne babu, sai wannan azurfan,"
yakalli azurfan sannan yace. Talaka bazai taba saka azurfam dubu arbain ba, tayi shiru lalle
yusuf yawuce tunaninta dole tanemo wani karya don azauna lafiya, donhaka tafara kuka, shiru
yayi yana kallonta, zuciyarsa na tafasa, meye kuma na kuka? Don kawai namiki magana?

Haba aliya !" Haka yata lallabi cikin kukan tace, "ni bansan iyayena ba, natashi agun wata antyna a
abj, anma iyayena yan garinnan ne. Toh antyn tamutu suka koreni yan gydan shine nadawo wannan gydan banawa bane, nata ne babu
hanyar ci da sha shine kawai naje nima aka kamani" har cikin ransa yaji tausayinta yakuma tausayinta tuni yace "zan yantaki, kuma zan
aureki" ido ta zaro sannan tace " kanaso ka kara tadamun hankali kasan cewa bazaa barka ba,
dan sarki dole sai yar sarauta, baba na manomi ne ta ina muke da sarauta, dariya yayi sannan
yace "ni mai ruwana , inasonki abunda nasani kenan, kuma bawanda zai hanani aurenki, balle
jikina nabani ke matata ce," aliya tace "toh nidai kayi hakuri kabarni nasamu naci, kuma ba sonka
nakeba donhaka kayi hakuri" dariya yayi yasan tafada ne, hartamike zata fita yace.

Tsaya!, yakaraso gefenta tana tsaye tana tunanin mezaice don hankalinta bai kwanta dashiba,
"jiya me abdullahi yamiki? Inace bai
rungumekiba? Daure fuska tayi tareda cewa "meya kawo runguma?* kamanta yanada wacce yakeso har
anyi tambaya?, meye na zargin?" Yayi murmushi "toh ai All men cheat, saidai kawai girmanki da
darajarki zai gwada, inhar yabari kikasan yana neman wata, toh bai daraja kiba, anma mai sonki
ko zaki mutu bazaki saniba, so bawani abubane don yaganki yace yanaso," bata kulashiba zata
fice saiyacigaba " kinga kaman ni ko ina neman wasu ba damuwa tunda kece major share holder aiba damuwa, " tasan har ranshi yafada, sabida yusuf nada neme neme, hakan yake tsorata ta kodai itama jikinta yakeso! Namiji ba a iya.

masa, gashi tafara sonsa, kyaunsa da takurinshi ya sa tafara sonsa, son da bata tabayiwa wani da
namijiba, wanda inhar tana tare dashi takan manta duk wani bakin cikinta shiyasa take taka tsantsan dashi domin kuwa yusuf zai iya
ruguza mata plan dinta, matsalan shine yusuf ne namiji data fara so take kauna, har daki tunani takeyi
ina mafita? Yazatayi? Kodai zata gudu tabar fadane? Toh gashi tanason ta gyra zaman yakolo
da falmata don yakolo tana cikin hatsari, toh itadai yazatayi?? Gashi batada abokin shawara, tayi missing iyayenta sosai kuka tayi sosai kaman ranta zaifita har aka kira azahar alokacin tayi sallah anma idonta ya kumbura bilki ta bukacivsukai abincin rana inyaso inta dawo taje gunvyakolo, anma aliya taki, koda bilki taje haka tadawo bayadda ta iya tanufi fannin, yana zaune haka tagama zubawa yana kallonta ganin idonta ya kumbura tuni ya ce meya samekk? Bata amsabba wanda hakan yasashi kara birkicewa, aliya
meya sameki?" Bata bashi amsaba sai taji wani sabon kuka, hannunta a fuskanta tuni yaga hannunta a kumbure ma, nan da nan yarude
first aid box yadauko yayi dressing hannun, yasa bandage har lokacin hawayen ne ke zuba, yayita
rarrashinta hartayi shiru, wani irin sonta ne ke tsuma shi, yace mezanmiki kiji dadi kidena
wannan kukan?" Tayi shiru sannan taja numfashi sannan tace "karka yantani, karabu dani kuma
ka manta dani".....

0 Response to "[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Bakwai"

Post a Comment